Kungiyar Avengers dai ta yi kaurin suna a yankin Naija Delta wurin fasa bututun mai da yin garkuwa da ma’aikatan sashen mai.
Bayan ta ajiye makamai kuma ta bayyana aniyarta na yin sulhu da hukumomin kasar a baya, kungiyar ta Avengers ta fitar da wata sanarwa a baya-bayan nan inda take bayyana aniyarta na sake komawa ga hare haren data saba kaiwa a sansanonin kamfanonin mai a yankin Naija Delta.
Manjo Ibrahim Abdullahi, shine kakakin hadakar rundunar tsaro dake aiki a yankin Naija Delta, kuma yace, sun yi damarar tinkarar duk wanda zai shirya ayyukan ta’addanci a wannan yanki. Kakakin rundunar tsaron ya kyautata zaton yin nasara a kan duk wanda zai tada fitina, ganin yadda rundunar ta kafa jami’anta a kowane bangaren yankin Naija Delta.
Su kuwa mutane yankin cewa suke yi, idan Avengers tana aikata miygun ayyuka, gwamnati kuma tana da laifi wurin gaza kulawa da al’ummar yankin. Wani da ya zanta da Muryar Amurka yace idan aka yi.
Your browser doesn’t support HTML5