Kungiyar Arsenal tana zawarcin dan wasan baya, wanda zai maye mata gurbin dan wasan ta Shkrodan Mustafi, sai dai ana ganin Arsenal ta mai da hankalinta kan sayen dan wasan baya na Barcelona Samuel Umtiti.
Arsenal, tana zargin cewar Shkrodan Mustafi, yayi sake wajen shigar kwallo a ragar kungiyar, a wasan da su kayi da Wolverhampton inda aka doketa 3-1 cikin wasan firimiya lig na bana a satin da ta gabata.
Bayan da magoya bayan kungiyar su kayi korafi akan dan wasan kocin kungiyar Emery ya fito ya kare dan wasan kan zargin, sai dai hakan ba zai hana shi neman sabon dan wasan baya ba.
Kocin na Arsenal ya amince da cewar kungiyar tana bukatar sake sabon shiri, na gyara kuma a bangaren baya ya kamata ta fara gyara idan har tana son yin abin arziki a kakar wasa mai zuwa.
Barcelona dai ta shirya tsaf wajan sayar da Samuel Umtiti sakamakon yawan rauni da yake fama dashi, sai dai tuni ta sayi dan wasa Linglet daga Sevilla wanda shine ya maye gurbin na Umtiti a wannan kakar.