Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta yi kira ga hukumomin Najeriya, da su mutunta ‘yancin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, da suka shafi damar yin walwala da fadin albarkacin baki.
Kungiyar ta Amnesty ta yi kiran ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, bayan da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya cire sarkin daga mukaminsa ya kuma sa aka mayar da shi jihar Nasarawa, inda aka yi mai daurin talala.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da Isa Sanusi jami’in hulda da jama’a na kungiyar Amnesty International a Najeriya, ya ce halin da aka sa Sarki Muhammadu Sanusi a ciki bai dace ba kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Jami’in kungiyar ya kuma ce Najeriya ta sanya hannu a wasu kudurori da yarjeniyoyi da yawa na kasa-da-kasa bayan haka kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kowanne bil’adama ‘yancin ya je inda ya ga dama ya kuma fadi albarkacin bakinsa. Amma a halin da ake ciki yanzu, ya kasance an tauye wa sarki Muhammadu Sanusi wadannan hakkokin.
“Shi ya sa muke kira ga gwamnatin Najeriya da ta bar sarkin ya yi walwalarsa, idan kuma ana zargin sa da wani laifi ne, to sai a gurfanar da shi gaban kotu,” a cewar Isa.
Ya kuma jaddada cewa kungiyar Amnesty International ba ta shiga harkokin siyasa sai dai abin da ya shafi harkokin bil’adama. Game da batun ala’adar gargajiya da ta shafi sarauta kuma, Isa ya ce ba za a yi shiru akan abin da bai dace ba, da abinda ya saba wa doka.
Ga cikakkiyar hirar da Mahmud Lalo yayi cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5