Kungiyar Amnesty ta ce Akalla Mutane Dubu 7 ne Suka Mutu a Tsare a Najeriya

Sojojin Najeriya.

Wata kungiyar dake hankoron kare hakkokin bil’adama ta fadi cewa ‘yan Najeriya fiye da dubu 8 suka mutu sanadiyar kokarin da gwamanti ke yi na murkushe mayakan sa kai na boko haram.

Kungiyar Amnesty international tace masu yi mata bincike sun gano cewa an kashe mutane fiye da dubu 1 da 200 ne aka kashe a samamen da sojojin Najeriya suke kaiwa tun shekarar 2009. Ta kuma ce akalla karin mutane 7,000 sun rasa rayukansu a lokacin da suke tsare hannun hukuma sakamakon azaba da kishirwa, da yunwa da kuma yanayin cinkoson jama’a a gidajen kason da aka ajiye su.

Kungiyar ta Amnesty international tace manyan jami’an sojan kasar sun sani sarai na yawan mutanen dake tsare, amma basu dauki wani mataki don hana cin zalin ba.

Kungiyar tayi kira ga sabuwar gwamanatin Najeriya, karkashin mulkin shugaba Mohammadu Buhari da ya kaddamar da bincike akan lamari.

Shugaba Buhari na ziyara a makwabciyar kasar Niger domin tattaunawa akan boko haram. Wannan ita ce ziyarar shi ta farko zuwa wata kasa tun da ya hau kujerar shugabanci.