Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto inda ta soki mahukumtar jihar Agadez da kakkausan lafazi saboda dauke wasu 'yan kasar Sudan fiye da dari da birnin ya yi zuwa wani yankin Madama wanda yake da matakan tsaro na soja.
Malam Risa Faltu magajin garin Agadez ya ce sun dauki matakan ne domin nisantar da al'ummarsu daga wasu miyagun dabiu da wasu cikin wadanda aka kai Madama ke aikatawa. Ya na mai cewa jama'ar Agadez jama'a ce mai son zaman lafiya. 'Yan Sudan din da aka kai Madama wasunsu na shaye shaye tare da aikata wasu abubuwan da basu dace da zaman lafiya ba.
Su ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam na jihar sun yi fatali da rahoton ita Amnesty International. Sun ce ba rahoto ya kamata ta fitar ba amma da wakilanta ta tura Agadez domin su gani da idanunsu abun dake faruwa, su kuma tattauna da hukumomin garin.
Malam Abu Nchua dan kungiyar kare hakkin dan Adam ne reshen jihar Agadez a cewarsa Amnesty International ta tafka kuskure dangane da zancen
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5