Kungiyar al-Qaida ta tabbatar da kashe shugaban kungiyar na biyu

Abu yahya al-libi

Madugun kungiyar al-Qaida, Ayman al-Zawahiri ya tabattarda cewa lalle an kashe shugaban kungiyar na biyu.

A cikin wani jawabin da yayi ta faifan bidiyo, Zawahiri ya yabi marigayin, Abu Yahya al-Libi, inda ya kara tabattarda cewa harin da wani karamin jirgin Amurka maras direba ya kai a kansa ne ya hallaka shi a yankin Arewancin Pakistan a cikin watan Yuni da ya gabata.

Marigayin, wanda haifaffen dan kasar Libya ne, ance shine yake jagorancin dukkan aiyukkan da kungiyar ta al-Qaida take gudanarwa a yankunan kabilun Pakistan da dama a lokacinda aka kashe shi.

A nan Pakistan ne dai sojan Amurka kuma suka kashe shi babban shugaban al-Qaida din, Osama Bin Laden a garin Abottabad a watan mayun shekarar 2011.