Harin ya fara ne da misalin karfe 10 na dare agogon yankin, yayin da wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wurin shakatawa na gabar teku mai yawan jama’a da suka je shakatawan dare.
Wasu hotunan bidiyo da aka kafe a yanar gizo daga wurin sun nuna mutane da dama kwankwance, wasu sun mutu wasu kuma sun samu munanan raunuka.
Bayan fashewar farkon, wasu ‘yan bindigan al-Shabab uku sun kai samame a dakin cin abinci da nishadi na bakin tekun.
Bugu da kari bayan kashe fararen hular, jami’an tsaro dake wurin sun kashe maharan, a cewar ‘yan sanda. Wani dan bindiga na hudu ya tarwatsa kansa, a cewar rahoto.
Nan da nan gwamnatin Somalia ta jibge rundunar tsaro domin fafatawa da maharan, a cewar shedu. Jami’an tsaron sun shaidawa ma’aikatar labaran kasar cewa sun dakile lamarin sa’o’I hudu bayan harin.
Asibitoci a Mogadishu sun yi kira ga taimakon jini domin ceto rayuwar mutanen da aka raunata a harin.
Al-Shabab ta saba kai hari a gidajen cin abinci da otal a bakin tekun Lido tsawon shekaru saboda wuri ne iyalai suka fi sha’awa, da matasa da ma mazauna kasashen waje da ke dawowa gida don yin cudanya da juna.