Kungiyar Al Shabab ta kasar Somaliya ta kwace wasu birane biyu

Sojojin Somaliya a harabar otel din Jazera a birnin Mogadishu.

Hukumomin kasar Somaliya sunce yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab sun kwace wasu birane guda biyu a kudancin kasar a jiya Asabar bayan da sojojin kungiyar kasashen Africa da ake cewa AMISOM a takaice sun janye daga biranen.

Hukumomin kasar Somaliya sunce yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab sun kwace wasu birane guda biyu a kudancin kasar a jiya Asabar bayan da sojojin kungiyar kasashen Africa da ake cewa AMISOM a takaice sun janye daga biranen,.

Haka kuwa ya faru ne kwanaki biyu bayan wani mumunan hari da yan yakin sa kai suka kai wani sansanin sojojin kungiyar kasashen Afrika da ya kashe sojoji Uganda da dama.


Mukadashin gwamnan yankin Shabelle Abdifitah Haj Abdulle ya fadawa Muryar Amirka cewa sojojin kungiyar kasashen Afrika sun janye daga sansanin El Salindi wani sansanin soja mai muhimmanci dake tazaa kilomita sittin kuda da Mogadishu baban birnin kasar.

Haka kuma yace a ranar Juma'a sojojin AMISOM suka janye daga wani gari.
Wani jami'in yankin yace rundunar AMISOM ta sheda mishi cewa yan yakin sa kai sun kutsa birnin yan sa'o'i bayan da jami'an tsaro sun janye daga birnin.

Yace wasu mazauna garin sai suka fara arcewa, yayinda wasu kuma suke cikin dimuwa da tsaro a saboda fargabar cewa kila yan yakin sa kai su kashe farar hula.