Kungiyar Al-Shabab Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai a Kenya

Sansanin Sojojin Amurka Da Na Kenya

Kungiyar ‘yan bindigar al-Shabab ta Somalia ta dauki alhakin kai harin jiya Lahadi a kan sansanin soji da rundunonin sojan Amurka da na Kenya ke amfani da shi.

Rundunar sojin Amurka a Afirka ta fada a rahotannin farko cewa an samu lalacewar kayan aiki da wasu gine-gine kuma lamarin ya yi muni. Tungar sojin dai yana a lardin Lamu ne dake kan iyakar Kenya da Somalia.

Wata sanarwar da rundunar sojin Amurka a Afirka ta AFRICOM ta fitar ta tabbatar da hayakin da ya turnuke sama ya fito ne daga kayan aikin da aka lalata da kuma ginin sansanin sojan.

Kwamishinan lardin Lamu Irungu Macharia ya tabbatar da harin ya kuma ce har zuwa yanzu ana zaman dar dar a wurin.

Ya ce "an kai harin ne tsakanin karfe hudu zuwa biyar a sansanin sojin dake karamin filin saukar jirage. Jami’an mu sun fafata da maharan har karfe shida. Ya ce amma yanzu kura ta lafa, amma kuma duk da haka hankali bai kwanta sosai ba da zamu je wurin." Sai dai kuma ya ce harkoki sun fara komawa yadda suke kana jamai’an su na wurin.

A wata sanarwa, al-Shabab ta ce tana rike da ikon yankin na sansanin ta kuma ce ta yi kisa da dama a wannan harin.