Wata kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta bayyana jin takaicin cewa kasashen dunya da sauran masu bada tallafi suna sakaci da tafiyar hawainiya wajen kai agaji ga dimbin mutanen kasashen Afrika dake fama da matsananciyar yunwar da Fari ya haifar musu. Kungiyar bada tallafi ta Oxfam da mazauninta ke a London ne take cewa wajibi ne akan kasashen da sauran cibiyoyi su cika alkwurran da suka dauka na kawo agaji don a samu sukunin tallafawa mutane kimanin rabin milyan da yunwa ke wa rayukkansu mummunar barazana a kasashen Somalia, Ethiopia da Kenya. Kungiyar ta Oxfam tace ita kanta tana da kudurin agazawa mutane kamar milyan ukku amma tana fuskantar karancin kudi kamar dala milyan 55 da take bukata don iya aiwatarda aiyukkan da tasa a gaba. Wannan rokon da Oxfam ke wa kasashe yana zuwa ne kwana daya bayanda Kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta bada sanarwar cewa a cikin makon gobe zata shirya babban taron bude asusun neman kudaden da za’a bada wannan agajin ga mutane sama da milIyan 12 da masifar ta shafa.
Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta koka dangane da sakaci da tace ana yi wajen talalfawa kasashen nahiyar Afrika dake fama da yunwa
Wata kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta bayyana jin takaicin cewa kasashen dunya da sauran masu bada tallafi suna sakaci da tafiyar hawainiya wajen kai agaji ga dimbin mutanen kasashen Afrika dake fama da matsananciyar yunwar da Fari ya haifar musu.