Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdulahhi Bala Lau ya ce yin haka ba zai haifar da da mai ido ba
WASHINGTON, DC —
Duk da cewa jam’iyar hamayya ta APC ta maidawa jam'iyar PDP mai mulki martani, kungiyoyin addinin Islama da masana na ci gaba da yin tir da Allah waddai da kalaman da jam’iyar PDP ta yi game da jam’iyar APCcewa akidar ta daya da jam’iyar ‘yan Uwa Musulmi ta kasar Masar kuma ta na da wani shiri na kawo siyasar bin addinin Musulunci da maida Najeriya kamar kasar ta Masar.
A wajen wani taron manema labarai kungiyar Izala ta bakin shugabanta Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta zargi yan siyasar Najeriya da neman fakewa da addini don cimma burin siyasa abun da ya ce ba zai haifar da da mai ido a Najeriya ba. Shi ma masanin ilimin kimiyar siyasa dakta Amuga Keptin Namala na jami'ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama ta Adamawa ya ce 'yan siyasar su yi hankali, su yi taka tsantsan, kuma su yi la'akari da abun da ke faruwa yanzu haka a kasar jamahuriyar Afirka ta Tsakiya. Wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5