Majalisar Wakilai ta tabbatar da tantance jakadu 40 wadanda za su wakilci Najeriya a kasashen waje kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito a yau.
Dama dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar sunayen jakadun 42 domin tantance su.
A cewar jaridar Punch, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kasashen waje Adamu Bulkachuwa ya bayyana cewa akwai wasu 'yan matsaloli da aka samu yayin tantance mutum biyu daga jihohin Neja da Yobe.
A cikin mutanen da aka tantance akwai 'yan jarida biyu, Debo Adesina daga Oyo da kuma Oma Djebah daga Delta.
An tantance yawancinsu ne ido na ganin ido, sai dai wadanda ba sa kasar dole aka tantancesu ta yanar gizo.
Ga kadan daga cikin jerin wadanda aka tantance.
Adamu M. Hassan (Taraba)
Abubakar D. Ibrahim Siyi (Bauchi)
Faruk Yabo (Sokoto)
Abubakar Moriki (Zamfara)
Paul Oga Adikwu (Benue)
Jazuli Imam Galadanci (Kano)
Dare Sunday Awoniyi (Kogi)
Ibrahim Kayode Laaro (Kwara)
Abioye Bello (Kwara)
Zara Ma’azu Umar (Kwara)
Mrs. Nimi Akinkugbe (Ondo)