"Kujerar Majalisar Tarayya Ba Ta Gado Ba Ce"

Majalisar Tarayya

A ranar hudu ga watan da ya gabata ne kotun daukaka kara da ke Kaduna ta soke zaben shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin tarrayya Alhassan Ado Doguwa, tare da ba da umurnin a sake zaben kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a jihar Kano bayan kwanaki 90.

Abin da ya dauki hankali shi ne duk da rinjayen da 'yan jamiyar APC ke da shi a Majalisar ba su zabi wani ya maye gurbin Ado Doguwa ba.

Yau uku ga watan Disamba ne take cika kwanaki 29 cif cif da majalisar wakilai ke gudanar da ayyukan ta babu shugaban masu rinjaye a bisa dalilin soke zaben Alhassan Ado Doguwa da kotun daukaka karar ta yi.

Shugaban sababbin 'Yan Jamiyar APC wato “APC CAUCUS” da ke Majalisar wakilai, Shehu Mohammed Wamban Koko, ya ce suna gudanar da ayyukan su babu shugaban masu rinjaye domin kansu a hade yake kuma shiri ne na cikin gida cewa a jira mai kujerara har sai bayan an sake zabe a Tudun Wadada da Doguwa a Jihar Kano tare da kyakyawar fatan zai ci zaben don ya dawo kujerarsa.

To sai dai ga lauya mai zaman kansa kuma masanin kundin tsarin mulkin kasa Yusha’u Waziri Mamman yana ganin yin haka ba daidai ba ne, domin kundin tsarin mulki ya tanadi barin kujera ga wanda ya ci zabe ne, ba abin gado ba ne da za a ajiye wa wasu shafafu da mai.

Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Medina Dauda ta aiko mana:

Your browser doesn’t support HTML5

MASU RINJAYI NA JIRAN ADO DOGUWA