Kungiyar matasa mai gwagwarmayar a ba matashi damar tsaya wa takaran mukaman siyasa da zara ya kai shekaru 18 ta dage da cimma burinta.
Burin nata ya samu karbuwa a majalisun dokokin tarayyar Najeriya. Baya ga samun goyon bayan na tarayya matasan sun samu goyon bayan majalisun jihohi fiye da 24 da doka ta tanada kafin a gyara kundun tsarin mulkin kasa ya amince da rage shekaru. Matasan sun samu jihohi 31.
Samun nasara a jihohi 31 ya nuna yanzu shugaban kasa ake jira ya sanya hannu ga kudurin ya zama doka.
Daya daga cikin shugabannin matasan Mike Amanza ya yi karin haske kan yawan shekarun da kudurin ya kunsa. Yanzu idan an kafa dokar duk mai shekaru 25 zuwa sama na iya tsayawa takarar majalisun dokoki da na wakilan tarayya. Daga 35 mutu na iya tsayawa takarar shugaban kasa ko gwamna ko zuwa majalisar dattawa.
Ahmed Dacada shi ma daya daga cikin shugabannin matasan ya lissafa matasa dake rike da mukamai daban daban a wasu kasashen duniya.
A saurari karin bayani daga rahoton Saleh Shehu Ashaka
Your browser doesn’t support HTML5