Kudin Da Mai Rabo Zai Ci A Tambolar Powerball Ya Kai Dala Miliyan Dubu Da Dari Uku

Yawan kudin da mai rabo ya ka iya samu a tambolar Powerball ta nan Amurka a ranar laraba mai zuwa, na ci gaba da haurawa sama, inda a yanzu, aka kiyasta zai kai dala miliyan dubu da dari uku, bayan da aka kasa samun wanda yayi nasarar harhada lambobin tambolar a ranar asabar.

Sai dai kuma, alkaluma sun nuna cewa akwai hanyoyi dabam-dabam na harhada lambobin tambolar har fiye da miliyan dari biyu da casa’in da biyu. Ma’ana, yiwuwar samun dukkan lambobi 6 da ake bukata domin cin babbar kyautar wannan tambola, sau daya ce a cikin miliyan dari biyu da casa’in da biyu.

Amma duk da haka, wannan bai kashe ma jama’a guiwar sayen tikitin wannan tambola wadda ake sayarwa a kan dala biyu kacal ba. Shugaban hukumar tambola ta Jihar Texas a nan Amurka, daya daga cikin jihohin dake cikin wannan tambola ta Powerball, Gary Grief, yace ya zuwa daren jiya lahadi, a kowane minti daya su na sayar da tikitin dala miliyan daya da dubu dari biyu na Tambolar Powerball.

Wannan kudin da za a iya ci na dala miliyan dubu da dari uku, ya ninka kudin Tambola mafi tsoka da aka taba ci a Amurka a baya har sau biyu, watau dala miliyan 656 da Tambolar Mega Millions ta bayar a ranar 30 ga watan Maris na 2012 ga wasu mutane uku da suka yi sa’ar iya harhada lambobin da suka ci tambolar a jihohin Kansas, Illinois da Maryland.

A can baya, kudi mafi tsoka da aka taba ci a Tambolar Powerball shine dala miliyan 590 da wani dan Jihar Florida ya ci a ranar 18 mayu 2013.

Ana buga tambolar Powerball sau biyu a mako, a jihohi 44, da Gundumar Colombia da kuma yankin Puerto Rico.

Kudin da aka iya ci a jibi laraba ya taru ne a saboda tun ran 4 Nuwamba babu wanda ya harhada dukkan lambobi 6 da ake bukata na lashe Tambolar. Da ma idan ba a samu wanda ya ci ba, to a kan hada kudin a kan tambolar da za a buga a gaba. Yanzu sau 18 ke nan ana bugawa babu wanda ya ci.

Sai dai duk da cewa babu wanda ya lashe babbar kyautar, an samu wadanda suka ci kananan kyaututtuka har na dala miliyan 160 a ranar asabar. Daga cikinsu, akwai tikiti biyu a jihohin Connecticut da Texas wadanda suka lashe dala miliyan bibbiyu saboda sun samu wasu daga cikin lambobin. Akwai kuma wadanda suka lashe dala miliyan daddaya a jihohi har 14.