Kudaden Shiga Na Gasar La Liga Ya Haura Arzikin Wata Kasa

An bayyana adadin kudaden da aka samu riba a gasar kwallon kafa ta La Liga, ta kasar Spain a matsayin mafi yawa da ta samu cikin kakar wasa guda, a tarihin kafa gasar.

Kididdigar da aka yi a shekarun 2017/2018 ta gasar kwallon kafar ta Spain sun bayyana cewa kudaden shigar da aka samu a kakar wasan ya kai Euro biliyan €4 da miliyan 479, sabanin shekarun baya na 2016/17 inda aka samu kudin shiga Euro biliyan €3 da miliyan 600.

Hakan ya nuna cewa, yawan kudaden shigar da gasar ta La Liga ke samu a shekara guda ya karu da kusan kashi 21%.

Bayan haka kuma, rahoton wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, gasar ta La Liga ta samar da guraben ayyukan yi ga al'umma, inda akalla mutanen da suka sami aiki ya kai sama da dubu 185,000, bayan haka gwamnatin kasar Spain na samun kudaden haraji daga Laliga da yawansu ya haura sama da Euro biliyan €4 a kowacce shekara.