A ranar Juma’ar Easter, mabiya addinin kirista sun yi imani da cewa rana ce da aka kashe Yesu Almasihu, wanda tashinsa daga matatattu ya kasance sanadin ceto daga hallaka da kuma alkawarin rayuwa na har abada da kaucewa shiga wutar jahannama ga duk wanda yayi imani da Isa Almasihu.
Rabaran Bakari Ibrahim ya ce Easter na cikin ginshikan koyarwa da abin da mabiya addinin kirista suka fi bada fifiko a kansa.
Mabiya addinin Kirista a fadin duniya kan gudanar da bikin Easter daga ranar Juma’a zuwa Litinin, kuma sau daya a kowacce shekara domin tunawa da mutuwa da tashin Yesu Almasihu, sai dai ba wai suna bikin rana ko lokacin da ya mutu bane.
Madam Lami Ibrahim dake koyarwa a cibiyar tauhidi a birnin Jos ta ce Easter na da muhimmanci sosai a rayuwar kirista.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5