Yau litinin wata kotu a birinin Legas ta yankewa wani matashi mai suna Fredrick Aghedo mai shekaru 28 hukuncin daurin shekaru hudu a sakamakon kama shi da tayi da laifin sayar da tabar wiwi.
Mai shari'a Saliu ya yanke wa matashin hukunci ne bayan amsa laifin safara da sayar da miyagun kwayoyi. Laifin sara da sayar da miyagun kwayoyi babban laifine da ka iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Alkalin ya bayyana cewa ya sassauta wa Aghedo hukuncin ne saboda wannan shine karo na fari da aka taba kama shi da laifin, dan haka kotu bazata iya gani sa'annan ta kyale laifin sayar da kwayoyi ba ganin yadda lamarin kema al'umma illa.
Mai shari'ar ya bada umurnin hanuntawa jami'an hukumar safara da sahan miyagun kwayoyi ta kasa kwayoyin domin lalata su., mai shigar da karar ya bayyanawa kotun cewar matashin ya aikata kaifinne tun ranar 21 ga watan yunin shekarar da ta gabata.
Daga karshe ya bayyana cewar an kama matashinne da adadin tabar wiwin da nauyin ta ya kai kilogiram 9, a unguwar Idiroko dake jahar Legas.