Koyan Sana'a Hanyar Fita Talauci

Abun wuya na murjani

Broadcasting Board of Governors da Muryar Amurka sun shirya taron kara ma juna ilimi a fannin kasuwanci da cinikayya ma matasa a Najeriya daga ranar 26 zuwa 30 na watan Satumban da ya gabata

A cikin shekaru da dama rashin aikin yi na cikin matsalolin da ake fuskanta wanda kuma yana cikin abubuwan da suka haddasa matsalar tattalin arziki.

Mataslolin kuma sun hada da hawa hawan farashi da wuyar biyan basuka da yadda ake samun karuwar rashin aikin yi kulluyaumin.

Hukumar kidigdiga ta sanar cewa akwai kimanin mutane miliyan 74 da suke neman aiki. Amma babu ayyukan gwamnati da zasu kwashe duka wadanda suka gama karatun jami’o’o da wasu manyan makarantu kowace shekara. Bugu da kari Najeriya ta shiga cikin tabarbarewar tattalin arziki.

Masana sun ruwaito cewa daya daga cikin hanyoyin da gwamnatin tarayyar Najeriya zata fita daga kangin tabarbarewar tattalin arziki shi ne ta kirkiro cinikayya. Ta hakan ne matasa kan iya kirkiro ayyukan yi. Misali, wata Maryam Inusa tayi nasara ta hakan.

Maryam ta tattauna akan yadda ta fara. Tace “na fito ne daga jihar Kogi kuma iyaye na talakawa ne saboda haka da kyar na je makaranta. Da na kammala makarantar sakandare na nemi shiga kwalajin kimiya da fasaha dake Idah. Na samu shiga kuma na koyi ilimin shakatawa na aikin otel da yawon bude ido. Allah Ya taimakeni na gama karatuna har na koyi yadda ake abun wuya na mata da murjani”

Maryam yace ta koyi yin abun yuwa domin tana da sha’awar kirkiro abubuwa masu kyau. Tace “ni wata ce mai son abu mai kyau, mai ban sha’awa, murjani kuma ya bani zarafin kirkiro abu mai ban sha’awa”

Tace “kodayake aikin abun wuya nada cin lokaci amma idan an gama kwalliya na biyan kudin sabulu”

Dangane da ribar da take samu sai Maryam tace “yawancin lokuta murjanai nada tsada amma abun mamaki shi ne "nakan saka jari kadan wajen sayen kayan aiki amma idan na gama nakan sayar akan kudi masu yawa. Misali idan na saka jarin nera 2,500 wurin sayen kayan aiki nakan samu nera 7000”.

Ta bayyana irin kayan aikin da take saye kamar su zaren kamun kifi da mashin da almakashi da dai sauransu.

Maryam ta kara da cewa tana anfani da ribar da take samu wurin kara ma kanta ilimin wasu ayyukan saboda tayi amannan cewa bai kamata mai sana’ar cinikayya ya tsaya kan sana’a daya ba. Tace ilimin yin abun wuya ya koya mata dinkin.

Yanzu dai ita Maryam tana aiki a wata makarantar horaswa da ake kira “Magvoile”. Tace “na koyi yin ado a makarantar na tsawon wata shida". Bayan ta gama ne ta nemi aiki a makarantar. Ta nunawa mutane wasu nata samfarin dinkin da tayi.

Tana cikin nuna samfarinta ne wasu kwastamominta suka shigo shagwanta su duba abubuwan da ta dinka.. Wata Mrs Jonathan tace ina son dinkinta shi ya sa kodayaushe nake zuwa wurinta. Ita ma Miss Jane tace tana sha’awar yadda take hada abubuwa kamar su yaduka.

Mataimakiyar manajar Magvoile Mrs Ernest Essein tace “Maryam tana da hazaka da iya kirkiro abubuwan ban sha’awa.

Wadanda suka shirya wannan koyin su ne

GRACE HOSEA TABULE

IDOKO ADOLPHUS

SULIMAN ALIYU

AISHA ALLYS SURKO