Wani yaro dan shekaru 16 a nan kasar Amurika, da aka haifa da wata irin matsala wadda take dakile basirar yara, ya yai wata rawar gani.
Shidai wannan yaron me suna Malika, ya kasance bai fara magana ba har sai da yakai kimanin shekaru 5 wanda kuma baya fahimtar kome aka koya masa, amma daga bisani bayan ya kai wani matakin rayuwa, ya kirkiri wata hanya da take taimakama yara da malamai wajen fahimtar karatu a saukake.
Wannan tsarin nashi da yakira “Gwarzon Duniya” wato abun da yake nufi shine kowane yaro na iya zama wani abu musamman idan ya lura da yadda rayuwa ke gudana. Sai yace, kowane yaro ya tashi da zummar cewar zai yi abu don taimakama wani badan kanshi ba, tahaka zai iya zama gwaro da kowa zaiyi kokarin koyi da.
Babban abun la’akari dashi a nan shine, yakamata iyaye da malamai su maida hankali wajen koyar da yara wasu darussa da zasu kara samusu kaimi wajen neman zama wani abu. Misalli kamar koyar da Tarihi, Labarai kamar su tatsuniya, al’adun wasu kabilu da kasa, da dai sauran maka mantan su, ta haka za’a iya samun dai-daito wajen zaburar da yara su zama wani abu a rayuwar wasu yaran.