Kotunan Sauraren Korafe-korafen Zabe Sun Fara Aiki

Wasu jami'an zabe na tattara sakamakon zabe a birnin Yola na jihar Adamawa, Fabrairu, 24, 2019.

Bayan kammala zabuka a Najeriya, alkalan kotuna na musamman da aka kafa domin saurarom shari’un zabe sun fara aiki a jihohi daban daban na kasar.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasar ke fatan alkalan sun kamanta adalci, yayin da masana dokoki da shari’a ke ganin kwaskwarimar da aka yi wa dokokin da suka shafi yanayin aikin kotunan zai ba su damar gudanar da hukuncin cikin hanzari.

Tun a cikin watan Fabrairun bana mai rikon mukamin babban jojin Najeriya ya rantsar da alkalan da za su saurari korafin zaben wadanda aka zabo su daga manyan kotunan tarayya da na jihohi da kotunan daukaka kara na shari’ar Musulunci da na customary.

A karkashin tsarin, akwai kotunan da aka kebe za su saurarin shari’un da suka shafi korafi akan zaben shugaban kasa sai na zaben gwamnoni kana da wadanda aka dorawa alhakin lura da shari’un ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jiha.

Dr Nasiru Adamu Aliyu Malami a tsangayar nazarin aikin lauya a jami’ar Bayero Kano ya ce kwaskwarimar da aka yi wa wasu sassan kundin tsarin mulkin Najeriya masu nasaba da shari’un zabe da gyaran wasu bangarori na dokar zabe, wani ci gaba ne a tsarin tafikar da shari’un zabe.

Tun bayan da Najeriya ta koma tafarkin dimokaradiyya shekaru 20 da suka shude, zargin cefanar da hukuncin shari’ar zabe ke yawo akan alkalan kasar.

Bayanai sun nuna yanzu haka, akwai kararraki fiye da 30 a gaban kotun shari’ar zabe ta jihar Kano wadda ake sa ranza za ta fara aiki gadan-gadan a makon da muke ciki.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotunan Sauraren Korafe-korafen Zabe Sun Fara Aiki- 3'39"