Kotun Sojoji ta Fara Shari'a a Kan Mutane Biyar a Somalia

Sojojin Somalia

Masu shigar da kara a Somalia sun tuhumci wasu mutane biyar da hannu a cikin wani harin bam da aka kai da wata babbar mota a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata a babban birnin kasar Mogadishu inda aka kashe mutane 512, harin ta’addanci mafi muni a tarihin nahiyar Afrika baki dayanta.

Mutane hudu a cikin wdanda ake zargin suna hannu hukuma ne, kuma sun bayyana gaban wata kotun sojoji jiya Litinin a Mogadishu, yayin da mutum na biyar kuma ya gudu.

Acikin wadanda ake tuhumar har da Hassan Aden Isak, mutumin da ake zarginsa da tuka motar da ake zaton an so ayi anfani da ita wajen kai harin kunar bakin wake na biyu a wannan rana.

Haka kuma Shugaban kotun sojojin Col. Hassan Ali Nur Shute ya zargi Isak da shirya kai harin da kuma zama babban madugun sashen kula da makamai da gudanarda kashe-kashen gilla na kungiyar al-Shabab a birnin Mogadishu.

Hukumomin Somalia dai sunce basa da wata shakka akan cewa kungiyar al-Shebaba ce ta kai wannan mummunan farmakin koda yake itra kungiyar har yanzu bata dauki alhakin kai harin ba.