Kotun Rwanda Na Tuhumar Paul Rusesabagina Da Shirya Muggan Laifuka Kan Farar Hula

Wata kotun kasar Rwanda na tuhumar wani mutum, wanda dalilinsa ne aka yi fim din nan mai taken “Hotel Rwanda,” da aikata ta’addanci, da hadin baki a yi kisa, da kuma kafa wata kungiyar ‘yan tawaye masu gwagwarmaya da makami.

Masu gabatar da kara sun zargi Paul Rusesabagina da shirya muggan laifuka kan farar hulan kasar Rwanda, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, a 2018.

Rusesabagina ya ki amsa cewa ya aikata wadannan laifuka bayan da aka tuhume shi da su jiya Litinin, ciki har da cewa ya na da alaka da kashe-kashen gilla, yana mai cewa wasu daga cikin tuhume tuhumen ba su ma da tushe.

Rusesabagina, wanda aka tsare tun zuwa karshen watan jiya, ya bukaci a sake shi bisa dalilai na rashin lafiya. Kotun za ta saurari bukatar belinsa ranar Alhamis.

A fim din na “Hotel Rwanda” ana bayyana Rusesabagina, wanda tsohon manajan otal ne, a matsayin gwarzo, wanda ya kare ‘yan kabilar Tutsi da ke guje ma kisan kare dangi na 1994.

An dauke shi a matsayin wanda ya ceci rayuka sama da 1,000.