Kotun Rasha Ta Umurta Tsare Wasu Ma'aikatan Jirgin Ruwan Ukraine

Jami'in leken asirin Rasha yana shigar da matukin jirgin Ukrain kotu

Wata kotun Rasha a Crimea ta bada umarni a tsare ma’aikatan jirgin ruwan Ukraine 12 a cikin mutane 24 da aka kama a ranar Lahadi a kan tekun Rasha, na tsawon watanni biyu.

Rasha tana zargin matukan jiragen ruwan sojojin Ukraine ne da shiga ruwan tekunta ba bisa ka’ida ba da kuma yin watsi da kashedi da jami’an tsaron ruwan Rashan suka yi basu, wasu zargi da Ukraine din ta musunta.

Ukraine ta kafa dokokin soji a kan iyakokinta na yankin a matsayin martani kan abin dake faruwa ta kuma kira ga sauran kawayenta a nahiyar turai da sauran kasashen yammacin duniya su kara kakabawa Moscow wasu takunkumai a kan Moscow.

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko yace dokar zata taimakawa karfin tsaron kasarsa a cikin wannan karin tashin hankali wanda kuma yayi daidai da dokokin ruwa na kasa da kasa, lamarin da zai dakile rikicin da Rasha ke yi a yankin.

Babban sakataren Majalisar Dikin Duniya Antonio Gutterres ya yi kira ga Ukraine da Rasha a jiya Talata da su kai zuciya nesa domin kaucewa kara dagula al’amura a yankin.