Kotuna Na Musamman Ne Zasu Taimaka a Yaki da Zarmiya a Najeriya

EFCC

Sau tari idan an gurfanar da wani a gaban kotu akan cin hanci da rashawa babu mamaki kotun ta sakeshi ko kuma ta bada beli daga bisani karar ta sukurkuce

Lamarin asusun Patience Jonthan matar tsohon shugaban kasar Najeriya dake bankin Skye dauke da Dalar Amurka miliyan biyar da dubu dari tara ya zama kwan gaba kwan baya biyo bayan sake umurnin da babban kotun tarayya ta Legas ta bayar.

Da farko Patience Jonathan ta ci nasarar cire dala dubu dari daya kuma idan da bankin dana kudin da ta cire duka a ranar da ta je bankin.

Yanzu dai EFCC ta mayar da hankali akan wasu dake da ajiya kuma suna da alaka da Patience Jonathan. Kotun ta tsayar da ranar 15 ta watan gobe ta zama ranar kariya ga duk wadanda ake tuhuma cikin shari'ar.

Kakakin fadar Shugaba Buhari, Garba Shehu yace da ma sake bude asusun Patience wani koma baya ne na wani dan lokaci ga yaki da cin hanci a Najeriya.

Yace ai can baya ma ba'a taba samun tsatsauran hukumci ba inda za'a ce ga wani gwamna an daureshi kamar yadda ya faru a jihar Adamawa. Yace a da wani ma ya fi karfin a je a tambayeshi bisa abun da ya aikata. Amma a wannan lokacin da ake kokari a yaki zarmiya sai kuma ga kotuna suna watsi da kararrakin. Yace dole a samu damuwa.

Inji Garba Shehu dalili ke nan da Mataimakin Shugaban kasa ya kirawo taron gaggawa da ya hada da Atoni Janar na kasa da shugabannin hukumomin bincike kamar EFCC, DSS, da ICPC domin a ji ta bakinsu inda matsalar take.

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci Ibrahim Magu ya nuna damuwa kan da yadda kotuna ke tafiyar da zargin almundahana da kawo cikasa ga zargin zarmiya.

Ibrahim Magu yace babu wani dan boko da zai saci kudin jama'a a barshi ya ci sai dai idan basu sani ba.

Masana shari'a da dama nada ra'ayin kafa kotuna na musamman ne kadai zasu iya shari'un satar dukiyar gwamnati da hukumcin da ya dace kuma kan lokaci

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotuna Na Musamman Ne Zasu Taimaka Wurin Yaki da Zarmiya a Najeriya - 2' 46"