A yau litinin Kotun kolin Najeriya ta dage bitar hukuncin da ta yanke na soke zaben gwamnan jihar Zamfara Shehu Kogunan Gusau na jam’iyyar APC inda ta mika ragamar ga gwamnan da ke kan gado Bello Matawallen Maradun na jam’iyyar PDP.
Tun farko an dage sauraron shari'ar ne don kammala dukan ka'idodin da su ka shafi masu hannu a shari'ar, amma duk da haka rashin shigowar jagoran lauyoyin APC na jihar Zamfara, ya sanya kotun ta kara dage shari'ar zuwa 17 ga watan Maris.
Kogunan Gusau da jam’iyyar APC na bukatar kotun ta sauya hukuncin farko da ya kawar da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC bisa rashin gudanar da zaben fidda gwani yadda ya dace.
Sani Gwamna kakakin jam’iyyar APC na Zamfara ya fadi cewa "za mu yi nasara da yardar Allah."
Lauya mai zaman kansa a Abuja, Buhari Yusuf, ya ce APC na da hurumin bin kadin karbe mata mulki a jihar ta Zamfara don ta ci zaben ta hanyar kuri’a.
Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun ya sha gargadin tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari da ya daina zafafa siyasar jihar.
Mai taimakawa gwamnan kan harkokin maneman labarai Zailani Bappah, ya ce su na da kwarin gwiwar samun nasara.
Haka zalika jam’iyyar PDP a jihar Imo ta shigar da bukatar bitar hukuncin da ya kawar da Emeka Ihedioha ya kuma ba Hope Uzodinma na jam’iyyar APC.
Ga cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5