Kotun Kolin India Ta Ba Mabiya Addinin Hindu Wani Fili Da Akayi Takaddama Akan Sa

A yau Asabar Kotun kolin kasar India ta ba mabiya addinin Hindu wani fili da aka yi ta takaddama akansa, abinda zai sa yanzu a fara gina wani wurin ibada a garin Ayodhya dake arewacin India, inda wasu tsagere mabiya addinin na Hindu suka lalata wani masallaci sama da shekaru 25 da suka wuce, tun a karni na 16 aka gina masallacin.

Ba tare da wata jayayya ba, hukuncin da aka yanke akan daya daga cikin dadaddiyar takaddamar da aka yi a kasar tsakanin bangaren ‘yan Hindu da Musulmai, kwamitin alkalan da suka yi zaman yanke hukuncin su 5, ya bada umurnin a ba musulman wani fili da ban don su gina masallaci a wurin.

A shekarar aluf dari tara da cisi'in da biyu aka fara takaddamar da aka kwashe shekaru sama da 20 ana yi akan eka 2.77 na fili, inda rushe wani masallaci a wurin ya haddasa tarzomar da tayi sanadiyar mutuwar mutane 2,000.

Shugabannin addinin Hindu da na musulman yankin sun jaddada yin kira akan tabbatar da zaman lafiya da kulla dangantaka mai kyau bayan da aka sanar da yanke hukuncin.