Kotun Koli Ta Tabbatarwa Da Ganduje, Tambuwal Mukamansu

Kotun Kolin: Ganduje, Tambuwal Su Ne Zababbin Gwamnoni

Magoya bayan Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, sun cika harabar kotun kolin Najeriya, domin nuna murnarsu dangane da hukuncin da Kotun ta yanke, wanda ya ce Ganduje da Tambuwal sun tabbata zababbun Gwmanonin Jihohinsu.

Sai dai Shugaban Alkalan Najeriya Tanko Mohammed bai halarci zaman ba a lokacin da kotun ta yanke hukuncin. Alkali Sylvester Ngwuta, shine ya jagorancin alkalai 4 a zaman hukuncin.

Jagoran lauyoyin Ganduje mai shari'a Ibrahim ya ce babu yadda za a yi a ce alkalai 14 sun yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Ganduje ya ci zabe a Kano, ya kuma ce idan aka duba hukuncin kotun sauraren koke-koken zabe, da na kotun daukaka kara, da na kotun Kolin, duk hukuncin daya suka bada.

A lokacin da ya ke nashi bayanin game da hukuncin, daya daga cikin lauyoyin dan takarar jam'iyyar PDP a Kano, Barista Umar Husseini Tudun Wada, ya ce sun rungumi kaddara tare da fatan za a hada kai domin a yi wa jihar Kano aiki, ganin hukuncin da Allah yayi ke nan.

A halin yanzu dai kotun kolin tana ci gaba da yin shari'a game da Jihohin Bauchi, Filato da kuma Benue.

Ga rahoto cikin sauti daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotun Kolin: Ganduje, Tambuwal Su Ne Zababbin Gwamnoni