Kotun Duniya Ta ICC Ta Bada Umurni A Cigaba Da Binciken Laifukan Yakin Kasar Burundi

A cikin sanarwar, alkalan sun ce, akwai hujjar ci gaba da binciken da ya shafi kuntatawa bil’adama.

Yau kotun bin Kadin manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba masu shigar da kara izinin gudanar da bincike akan zargin da aka yiwa gwamnatin kasar Burundi cewa, ta aikata laifukan yaki kan 'yan hamayya tsakanin watan Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha biyar zuwa watan Oktoba na shekarar dubu biyu da goma sha bakwai.

Alkalan sun ce laifukan sun hada da kisan kai, da fyade da ganawa mutane akuba da ta kai ga mutuwar mutane sama da dubu abinda ya sa mutane dubu dari hudu yin gudun hijira daga kasar.

An yake hukumcin ne ranar ishirin da biyar ga watan Oktoba, kwanaki biyu kafin Burundi ta tsaida shawarar janyewa daga kotun. Ba a bayyana shawarar da kotun ta yanke ba, sai yau alhamis, sai dai kotun tana da hurumin sauraran kararraki akan laifukan da aka aikata a Burundi ko tana matsayin memba ko babu.

An gudanr da zanga zanga dabam dabam a Burundi a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar bayanda shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da cewa zai nemi wa’adin mulki karo na uku. Masu kushewa lamura sun ce, yana watsi da wa’adin mulkin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, da kuma yarjejeniyar da ta kawo karshen yakin basasa a Burundi.