Kotun DR Congo Tayi wa Mutane 11 Daurin Rai da Rai Bisa Laifin Fyade da Kisa

Shugaban Kasar DR Congo

Shugaban Kasar DR Congo

An yankewa wasu yan kungiyar, ‘yan yakin sa kai na kasar demokaradiyar jamhuriyar Congo 11 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bisa laifin yiwa wasu yan mata da dama fyaden taron dangi da kuma kisa.

Kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama sun yabawa wannan hukunci a matsayin abin tarihi a kasar inda ake yawan aikata cin zarafin jima’I kuma ba a hukunta masu aikatawa.

An dade, masu aikata laifin fiyade a Congo suke tsamanin cewa ba za’a taba hukunta su ba, a cewar sanarwar da wata kungiya mai zaman kanta ta Physicians For Human Rights ta gabatar.

A cewar karar da aka shigar, shugaban kungiyar yan bindigan Batumike ya dauki malamin boka wanda ya bashi shawarar cewa yiwa yan mata fiyade, zai sa harsashi bai ratsa su ba. Karama a cikin wadanda aka yiwa fiyaden jaririya ce mai watanni takwas a duniya

An tubewa Batumike rigar kariyar da dokar kasa ta bashi a matsayinsa na dan majalisa domin a gurfanar da shi gaban doka.

Tashin hankali ya barke a kauyen Kavumu mai tazarar kilomita 25 daga birnin Bukavu a cikin shekarar 2013 kuma ya ci gaba shekaru da dama.

Kotu ta baiwa yan matan da aka yiwa fiyaden kowanensu dala dubu biyar kana kotu ta bada dala dubu 15 ga kowane iyalin da aka kashe musu mutane sabili da sukar ayyukan yan bindigar.


Ofishin Jakadancin Amurka ya fada a wani sakon Twitter cewa hukuncin kotu wani babban mataki ne ga shari’a da kuma mutunta hakkin bil adama a Congo.