Kotun Daukaka Kara Ta Tarayya Ta Hana Maido da Dokar Trump

Alkalan Kotun Daukaka Kara Judge William Canby - Judge Richard Clifton - Judge Michelle Friedland da suka haramta dokar Trump

Kotun daukaka kara ta tarayya jiya Alhamis, taki ta dawo da aiki da dokar da shugaba Donald Trump ya bayar na dakatar da ‘yan kasashen nan 7 wadanda galibinsu musulmai ne da yin balaguro zuwa Amurka.

Alkalan su 3 wadanda dukkan su daga Kotun daukaka kara dake Francisco suke, sun amince da hukuncin dakotun farko ta yanke wanda ya dakatar umurnin, ya kuma kyale wadanda dokar ta dakatar ci gaba da balaguronsu zuwa Amurka.

Suka ce “ mun yanke hukuncin cewa bamu ga alamu gwamnati zata sami nasara da hujjojin da ta gabatar a daukaka karan nan ba, haka kuma ta gaza nuna illa ko rauni da kasa maido da aiki da dokar zata kawowa mata ba.”

Sai dai shugaba Trump ya aika da sako a shafin sa na Twitter yana cewa “mu hadu Kotu domin ko tsaron kasar mu na cikin hadari,”jim kadan da yanke hukuncin.

Idan dai ba a manta ba a cikin makon jiya ne alkali James Robert dake gundumar Seatle ya bada umurnin wucin gadi na dakatar da umurnin da shugaba Trump ya bayar, bayan da jihohin Washington da na Minnesota suka shigar da kara kan wannan batu.