Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya ba Jegede damar tsayawa zaben gwamnan Ondo wanda za'a gudanar ranar Asabar 26 na wannan watan.
Shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar PDP Sanata Walid Jibrin yace zargin cewar bangaren shari'ar kasar ya lalace to bai lalace ba domin shari'a ta kawar masu da Modu Sheriff. Yace sun gyara masu shi. Yace mutanensu suna murna ba kadan ba.
Inji Jibrin alamomi sun nuna zasu ci zaben domin mutane suna murna da hukumcin kotun. Yace ko hukumar zabe ta kara lokaci ko kada ta kara ba dan takararsu, Jegede zai ci zabe.
Saidai Jibrin yayi tababan samun lokacin da dan takaran nasu yake dashi na cika duk takardun da ake bukata ya cika nan da ranar Asabar da za'a yi zaben. Yace da so samu ne to a kara masu lokaci.
Mutanen bangaren Modu Sheriff sun ce su basu ga hukumcin ba saboda haka ba zasu bayyana matakan da zasu dauka ba sai sun karanta hukumcin.
Hukumar zabe tace duk hukumcin da kotun ta yanke dashi zata yi aiki.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5