Kotun dake Tuhumar 'Yan Jarida na Al-Jazeera a Masar ta Dage Zamanta

'Yan jaridan Aj-Jazeera da ake tuhuma da goyon bayan 'yanuwa musulmi

Kotun da takamata ta yankewa 'yan jaridan kamfanin Al-Jazeera hukunci ta dage zamanta yau.

Yau Alhamis wata kotu a kasar Masar da dage zaman yiwa 'yan jarida na talibijan Al-Jazeera hukunci.

An zargin 'yan jaridan ne da baiwa 'yan kungiyar Muslim Brotherhood ko kuma kungiyaar 'Yanuwa Musulmi da gwamnatin kasar ta haramta goyon baya.

Kamfanin Al-Jazeera yace ya fusata matuka da dage yin hukuncin da kotun tayi. Da ta zauna kotun da ta yankewa Muhamad Fahmy dan asalin kasar Canada da Baher Mohamed dan asalin kasar ta Masar da Peter Greste dan asalin Australia hukunci.

Ana kyautata zaton kotun zai zauna mako mai zuwa

Wata kungiya mai zaman kanta tace 'yan jaridan aikinsu suke yi na yada labarai lokacin da aka cafkesu a watan Disamban shekarar 2013. Daga bisani aka ce an samesu da laifi. Alkalin da ya yi shari'a ya yiwa Greste da Fahmy daurin shekaru bakwai kowanne kana ya daure Mohamed shekaru goma.

A watan Janairu ne kotun daukaka kara yace a sake shari'ar domin lotun da ya dauresu ya kasa bada cikakken shaida cewa suna goyon bayan Muslim Broitherhood.