Kotun Da'ar Ma'aikata Ta Ce Sanata Saraki Ba Ya Bukatar Beli

  • Ibrahim Garba

Shugaban Majalisar Tarayyar Najeriya Bukola Saraki

Kotun Tabbatar Da Da'ar Ma'aikata ta ce Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya je gida ba tare da beli ba; ganin ya je kotun da kansa.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ki amsa dukkannin laifuka 13 da ake zarginsa da aikatawa kamar yadda akawun kotun ya karanta. Bayan an tafka muhawara tsakanin lauyoyin gwamnati da masu kare Sarakin, sai shugaban Kotun Tabbatar Da Kotun Ma’aikata Yakubu Danladi Umar ya ce tunda Sarakin ya zo kotu da kansa ya soke sammacin kama shi da ya bai wa Supeto-Janar na ‘yansanda.

A yanzu dai an dage sauraron karar zuwa ranakun 21, 22 da 23 na watan Oktoba.

A halin da ake ciki kuma, lauyan gwamnati Rotimi Jacob ya shaida ma wakiliyarmu Madina Dauda cewa ya yi farin ciki da yadda wanda ake zargin ya zo kotu da kansa, inda aka karanta masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa daya bayan daya. Ya ce wannan ne karo na farko da wani mai babban mukami irin haka ya gurfana a gaban kotu har aka karanta masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, al’amarin da ya ce ko ba kowai na nuna cewa ana samun cigaba.

Shi kuwa mai kare Shugaban Majalisar Dattawan Joseph Daudu ya ce an bi tsarin da ya kamata. Ya ce ko ba komai ba shi yiwuwa a daure wanda ya ke karewar ba tare da an bi kadi ba. Ya ce an ma ce Shugaban Majalisar ya tafi gida ba tare da bukatar beli ba.

Your browser doesn’t support HTML5

KOTUN DA'AR MA'AIKATA TA CE SANATA SARAKI BA YA BUKATAR BELI -3'03''