Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta yi watsi da karar da wata kungiya ta yi ta bukatar a hana gwamna Mohammed Jibrilla Bindow na jahar Adamawa sake tsayawa takara bisa zargin cewa wasu takardun shaidar kammala makaranta da gwamnan ke amfani da su na bogi ne.
Da ya ke yanke hukunci, mai shari'a Adeniyi ya ce kotun ba ta ma da hurumin sauraren wannan karar tunda wanda ake zargi da mallakar takardun jabun ba a yakin Abujan ya ke ba.
To amma baya ga wannan kara da wata kungiya, daya daga cikin 'yan takarar gwamnan jahar Adawa karkashin jam'iyyar APC ta su Bindow mai suna Dr. Mahmud Hailu Ahmad, shi ma ya shigar da kara makamanciyar wannan. Wato dai da sauran rina a kaba ga gwamnan Bindow.
Ga dai Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5