Wani alkali ya karawa wani ba'amarike karin wa'adin da zai zauna gidan kaso domin an sameshi da laifin kasancewa dan kungiyar al-Qaida
WASHINGTON, DC —
Wani ba Amurke Jose Padilla da kotu ta samu da laifin goyon bayan kungiyar al-Qaida, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 17 an kara masa shekaru hudu, domin wani alkali ya yanke hukunci jiya talata cewa an yi masa sassauci ainun.
Padilla dan shekaru 43 da haifuwa, wanda aka sameshi da laifi a 2007 a shari’ar da aka yi masa a jihar Florida dake kudancin Amurka, an kama shi ne a 2002 a tashar saukar jiragen sama dake Chicago, bayanda ya dawo Amurka daga abunda masu gabatar da kara suka kira sasanin horaswa na kungiyar al-Qaida a Afghanistan.