Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Mai Shekaru 20 Daurin Shekaru 15

Wata kotu ta yankewa wani matashi mai shekaru ashirin da haihuwa daurin shekaru goma sha biyar a sakamakon kama shi da aka yi da laifin balle kofa da satar kayan da darajar su takai yawan kudi Naira dubu dari takwas da tasa’in da takwas.

Kamar yadda mujallar Vanguard ta wallafa, mai gabatar da kara ASP Aibedion Obakpolor ya bayyana wa kotun cewar matashin tare da sauran wadanda ake zargi sun aikata wannan aika aika ne ranar 13 ga watan Maris na wannan shekarar a wani gida mai lamba 187, akan layin Sapele dake jahar Benin.

Mai gabatar da karar yace matashin mai suna Abubakar ya sacewa wata mata mai suna Mrs Uyi Benson kayan da adadin su ya kai yawan kudi Naira dubu dari takwasa da tasa’in da takwas ne, kuma ya kara da cewa laifin da Abubakar ya aikata ya saba ma kundin tsarin mulki sashi na 516 da kuma sashi na 413 na Najeriya.

Alkilin ya yanke ma Abubakar hukuncin daurin shekaru goama sha biyar ne a sakamakon laifuka uku da kotun ta tuhume shi da aikatawa.