Ana Tuhumar Wani Matashi Da Ya Lalata Karamar Yarinya A Kotu

A jiya talata ne aka gurfanar da Oluwaseyi Akinmulayo, wani matashi mai shekaru 37 a wata kotu da ke Ikeja a birnin lagos bisa zargin sa da aikata laifin yin lalata da wata karamar yarinyar da yake ruko.

Akinmulayo wanda ke zama a gida mai lamba 22, a layin Omorale Johnson, Lekki Phase 1, na fuskantar wannan tuhuma ne a yayin da ake zarginsa da aikata wannan laifi. A cewar jami'in dan sanda mai gabatar da karar Sajen Jimah Iseghede, matashin ya aikata laifinne a cikin watan fabarairun da ya gabata a gidan sa.

A cewar dan sandan, matashin ya yi anfani da yarinyar wadda yake ruko mai shekaru goma sha biyar kuma ya umurce ta da kada ta kuskura ta fadawa kowa.

Daga bisani yarinyar ta fada wa mahaifiyar ta inda shi kuma mutumin ya yi batan dabo bayan aikata laifin kafin aka yi sa'a aka cafke shi har aka kawo shi zauwa kotu a cewar jami'in tsaro mai shigar da karar.

Mai shigar da karar ya ce laifin da matashin ya aikata ya saba ma dokar tsarin mulki Najeriya mai lamba 137 na kotun aikata laifuffuka dake lagos.

Mai shari'ar Mr Tajudeen Elias ya bada belin mai laifin a kudi zambar naira miliyan biyu, Elias ya bukaci matashin ya biya kudi naira dubu dari biyu a ma'ajiyar kotun. daga karshe an dage sauraron karar har sai tara ga watan Satumba.