Kotu Ta Tabbatar Da Julius Abure A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour

Shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure

Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta jaddada cewa har yanzu Julius Abure ne shugaban jam’iyyar Labour na kasa.

A hukuncin da Mai Shari’a Hamma Barka ya zartar, kotun mai alkalai 3, tace hukuncin da ta yanke a ranar 15 ga watan Nuwamban 2024, wanda ya amince da Abure a matsayin shugaban jam’iyyar na nan daram kasancewar babu wata kotu da ta rushe shi.

Mai Shari’a Barka ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zartar da hukunci a kararraki 2 daban-daban da aka daukaka; wacce Sanata Nenadi Usman ta shigar da kuma wacce kwamitin rikon jam’iyyar da hukumar zaben Najeriya (INEC) suka shigar.

A yayin da yake korar karar saboda rashin hurumi, Mai Shari’a Barka yace kotun daukaka karar ta yi la’akari ne da hukuncin da ta yanke a baya na ranar 13 ga watan Nuwamban 2024 wanda ta tabbatar da cewa “har yanzu Abure ne shugaban jam’iyyar Labour na kasa.”