Kotu Ta Tabbatar Da Halaccin Kwamitin Rikon Kwarya na Jami’yyar APC

APC CARETAKER/EXTRAORDINARY CONVENTION PLANNING COMMITTEE

Jagororin kwamitin rikon Jam’iyyar APC sun fitar da sanarwa a hukumance kan hukuncin kotun koli na tabbatar da halarcin kwamitin riko na jam'iyyar APC

La'akari da ce-ce kuce da jam'iyyar ta yi ta fuskanta a yan kwanakin baya bayan nan dake nuni da cewa bai kamata kwamitin rikon ya shirya zaben shugabanin daga matakin gudumomi zuwa sama ba.

Kazalika Wannan sanarwa na zuwa ne bayan kiki-kaka da aka yi ta samu tsakanin mambobin jam’iyyar da ke neman kujeru da suka yi ta yada jita jitan cewa shugaban kwamitin kana Gwamna jihar Yobe Mai Mala Buni bai cancanci rikon jam’iyyar ba la’akari da matsayinsa na gwamna a bisa tanadin dokar jam’iyyar.

Masani shari’a kana daya daga cikin Mambobin kwamitin Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana sanarwar bisa hukuncin kotun koli da ya samu rinjaye daga mafi yawan alkalai wadanda suka karanta kuma suka yarda da hukuncin, kan cancantar kwamitin da kuma rike mukamai biyu a matsayin Gwamna da shugaban kwamitin rikon kwarya da Mai Mala Bunin ke yi.

hukuncin Kotun koli ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC stashi 13 sakin sashi na 3 (IV) da ya ba da damar nada kwamitin mai cikkaken ikon tafiyar da ayyukan jam’iyya

kamar yadda dokar kundin tsarin mulki na jam’iyyar PDP cikin sashi na 33 sakin sashi na 3 a shekarar 2012 ya tanadar, wanda ya kai ga babban taronta mai cikkaken iko, da har aka nada jagoranta Ali modu Sheriff a shekarar 2016, inda ya samu rinjaye a hukuncin Kotun

Dangane da wannan bayanai kwamitin ya yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka kai karar jam’iyyar kotu da su janye karar su tare da amfani da tsarin sulhu don magance korafe -korafen su tare da mai da hankali kan manyan taruruka da ke tafe don zaben sabin shugabanni da kuma tabbatar da an samu hadin kai da jittuwa a jam’iyyar

A daya bangaren gwamnoni yayan jam’iyyar APC mai mulki sun nuna goyon bayan su ga takwaransu na jihar Yobe kana shugaban kwamitin na rikon kwarya jam'iyyar Mai Mala Buni bisa tabbatar da mukamin nasa da kwamitin zartaswa na Jam’iyyar ya yi

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Tabbatar Da Halarcin Kwamitin Rikon Kwarya na Jami’yyar APC - Farfesa Tahir Mamman