Kotu Ta Samu Wasu 'Yan Pakistan 4 Da Laifin Da Ya Shafi Ta'addanci

Wasu shugabannin wata kungiyar mayaka masu tsattsauran ra’ayi ta Pakistan su 4, da ke da alaka da wasu munanan hare-hare da aka kai a makwabciyar kasar India, an tabbatar sun aikata laifin samar da kudaden ayyukan ta’addanci.

Wata kotu ta musamman da ke gabashin birnin Lahore ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis wanda ya gano cewa lallai mutanen su hudu sun aikata laifin tara kudade da kuma samar da kudade ba bisa ka’ida ba don ayyukan kungiyar Lashkar-e-Taiba, wadda kuma ake kira kungiyar LeT.

An haramta kungiyar ta LeT a Pakistan tun a shekarar 2002.

Jami'an Indiya da na Amurka sun zargi kungiyar da kitsa hare-haren ta'addancin da aka kai a Mumbai wanda suka yi sanadiyar kisan mutane 166 a shekarar 2008.

Ma’aikatar yaki da ta'addanci ta lardin Punjab, wadda ta gudanar da bincike tare da gabatar da kara, ta bayyana sunayen mutanen, Zafar Iqbal, Yahya Aziz, Abdul Rehman Makki da Abdus Salam.