Za a sake daukaka karar da wasu matasa suka yi, sakamakon korar karar su da aka yi na da'awar ka'idojin yanayi da gwamnati ta yanke cikin kankanin lokaci. Hakan kuma zai janyo tsaiko da ci baya na bibiyan hukuncin doka a madadin matasa da yancin su a cewar masanan.
Wani alkali ne ya kori karar da matasan suka shigar a kotun ranar Talata, inda suke jayayyar cewa dole ne Jihar Washington, ta kara yin wani abu domin rage sinadarin carbon da ke fita mai kashe itattuwa da fure, tare da janyo illa ga al'umma. Alkalin ya ce wannan lamari na 'yan siyasa ne ba na kotuna ba.
Hukuncin da alkalin ya yanke, shine karo na farko da kotu ta kori karar da matasa suka yi, suna bukatar hukumomi su kara himma wajen dakile matsalolin sauyin yanayi, inda suke cewa ana keta hakokin yancin da dokar kasa ta basu a cewar masanan. Wata Lauya dake aiki da kungiyar, Andrea Rodgers ta fadawa kungiyar Thomson Reuters Foundation cewa zasu daukaka kara.