Da yake gabatar da shara’ar alkalin alkalan jihar mai shara’a Nathan Musa ya ce kotu ta sami tsohon gwamna Barrister James Ngilari da aikata dukkan laifuffukan biyar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta tuhumeshi da su na ba da kwangilar sayan motoci ashirin da biyar kan kudi sama da naira miliyan dubu dari da sittin da shida ba tare da bin sharudan da hukumar ba da kwangila ta jiha ta shimfida ba.
Kwamishinan shara’a kuma jagoran lauyoyin gwamnatin jihar Barrister Silas Sanga ya ce ko da yake ba su ji dadin hukuncin ba akwai darusa da shugabanni da masu shara’a zasu koya daga sakamakon shara’ar.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa Mr. Ibrahim Walye daya daga cikin wadanda suka gurfana gaban kotu kuma ta wanke su kan laifuffuka hudu da ake tuhumarsu da su ya ce duk da cewa sun sami yancinsu suna bakin cikin dauri da kotu ta yiwa tsohon gwamnan.
Wannan hukunci na kotun inji wani mai sharhi kan lamuran da suka shafi shara’a kuma tsohon mataimakin magatakardan babban kotun jihar Adamawa Barr, Husseini Duraki Kazir ya ce wannan hukunci zai karawa alkalai kima a idon jama’a.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5