Bisa ga dukkan alamu kallo na neman komawa sama a jihar Adamawa inda wata kotu ta bai wa hukumar zabe INEC umarnin cewa ta dakatar da batun sake zaben da za ta yi a wasu rumfunan zabe har sai an kammala shari’a a karar da jam’iyar MRDD, wato "Movement for the Restoration and Defence of Democracy" ta shigar.
Jam'iyyar na kalubalantar hukumar zaben ne da rashin saka alamarta a kuria'r zaben gwamna da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata, watau jam’iyar na neman a rusa zaben domin a sa na ta dan takarar.
Jam’iyar dai ta shigar da karar ne a babban kotun jihar Adamawan inda Justice Abdul’Aziz Waziri ya ba da umarnin dakatarwar.
Sai dai kuma hukumar zabe INEC, ta ce a bisa dokar zabe da ake amfani da ita a yanzu musamman sashi na 8, karamin sashi na 10 cikin baka, umarnin kotu ba ta dakatar da zabe.
Ya kara da cewa INEC, ba ta da masaniya game da wannan umarni, a cewar kwamishinan hukumar zaben ta INEC a jihar Barr. Kassim Gana Gaidam.
Yanzu dai an zura ido a ga yadda za ta kaya kafin nan da ranar da hukumar zaben ta saka domin sake zabe a rumfuna 44.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5