Kotu Ta Dakatar Da Kafa Sabuwar Majalisar Masarautun Kano

Bukin Nadin Sarkin Tsibiri a Nijer Bubakar Marafa Kiassa

Ra'ayoyin jama'a sun bambanta a kan kafa sabuwar Majalisar Masarautu da gwamnatin Kano ta kafa biyo bayan kirkiro wasu sababbin masarautu hudu a jihar, a daidai sa'adda wata kotu ta dakatar da kafa majalisar.

Kwanaki uku bayan da gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta ayyana Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin shugaban sabuwar majalisar sarakuna ta jihar Kano, masu maraba da sabbin sarakunan da kuma masu hamayya da su, na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi

Sabuwar majalisar sarakunan ta jihar Kano ta kumshi dukkanin manyan sarakunan jihar su 5 da masu nada sarki guda 2 daga kowacce masarauta, Daraktan hukumar tsaro ta DSS da kwamishinan ‘yan sanda da wakilan ‘yan kasuwa da kwamishinan kananan hukumomi kana da shugabannin kananan hukumomin da ke karbar bakuncin fadar masarautun guda biyar da dai sauran masu ruwa da tsakai, kamar yadda yake kunshe cikin dokar masarautu ta jihar Kano.

Tuni dai gwamnatin jihar ta ayyana malam Muhammadu Sanusi 2 a matsayin shugaban majalisar

Malam Ibrahim Ado Kurawa, daya daga cikin makusantan fadar Kano kuma mai Nazari da bincike akan harkokin sarautun gargajiya, yana ganin wannan a matsayin sabon al’amari.

Ya ce “duk kasashen da aka kirkiro masarautu, ba inda a ka ce sarki na asali ya kasance a karkashin wani sarki sai a Kano da aka yi yanzu. Hakan na nufin za’a yi lokacin da Sarkin Kano zai kasance a karkashin Sarkin Karaye, da yake za’a rika jujjuyawa ne. Wannan ya sabawa hankali da tsarin da bature ya yi. Idan aka bar tsarin haka, ba sarkin Kano a ke ci wa mutunci ba”.

To amma Danmasanin Gaya, Alhaji Nura Kani na cewa, lamarin bai kai na tada jijiyar wuya ba.

“Abin da aka ce za’a yi karba-karba ne a sarakunan, in ka duba wannan wani tsari ne da aka yi shi kan doka. A da can an ce an yi ba bisa doka ba, to a yanzu an yi dokar kuma haka ta tsara, kuma aka fara da masarautar Kano. To ina wani laifi a cikin wannan?”

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da fadar Sarkin Kano ke cewa, har sai ta samu takardar gwamnati dake tabbatar da nadin sarkin Kano a kujerar ta shugabancin majalisar sarakunan jihar, sannan zata bayyana matsayarta.

Babbar kotun Kano ta bada odar dakatar da kaddamar da majalisar, kamar yadda masu nada sarki a masarautar Kano suka nema.

Ga karin bayani daga Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu ta ba da umarnin dakatar da sabuwar majalisar masarautun Kano