Kotun a karkashin mai shari'a A.T. Badamasi ta bada odar taka birki ga sarkin Kano da majalisarsa da antoni janar na jihar Kano akan cigaba da aikin.
Kotun ta hana duk wani yunkuri na rusa kowane bangaren fadar ko sauya wani gine-gine na tarihi a cikin gidan Sarkin Kano da ake yiwa lakabi da Gidan Rumfa.
Matakin kotun ya biyo bayan karar da Alhaji Salim Abubakar Bayero ya gabatar wanda ya yi korafin cewa sabbin gine-ginen wani salo ne na shafe ababen tarihin masarautar.
Barrister Sanusi Umar shi ne lauyan mai gabatar da kara. Yace fadar ta kai shekaru dari biyar kuma akwai wuraren tarihi har da makabartan sarakuna da matansu da yaransu. Yace shirin sarkin yanzu shi ne ya rushe wani bangaren fadar da ya hada da makabartar inda aka binne wanda ya kafa fadar Muhammad Rumfa.
Amma majalisar masarautar Kano ta bakin dan Majen Kano Alhaji Munir Sanusi tace batun yiwa fadar kwaskwarima a cikin tsarin sarautar Kano ba abu ne sabo ba domin ko a can baya wasu sarakunan Kano sun sauya wasu sassa na fadar saboda tsufansu. Ya bada misali da garambawul da aka yiwa kofar kudu da kuma kofar arewa.
Amma masana harkokin shari'a gani su ke yakamata iyayen kasa su dinga gujewa duk wani abun da ka sa a gurfanar dasu a gaban kuliya domin tsira da mutuncinsu. Daga ranar da suka zubar da mutuncinsu to basu da wata daraja kuma a idanun jama'a saboda dokar kasa bata basu wani kariya ba illa kiman da jama'a ke basu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5