Kotun dake sauraron karar mutanen ashirin da hudu da ake zargi da hannu kan kisan tsohon hafsan sojan na Najeriya, Janar Idris Alkali, ta dage sauraron karar zuwa ranar goma sha uku ga watan Fabarairun wannan shekarar.
Ana zargin mutane ashirin da hudun da mallakar makamai, zagon kasa da kuma hallaka Janar Idris Alkali a shekarar da ta wuce.
Alkalin kotun mai shari’a Daniel Longji, bayan ya saurari bahasi daga bangarorin masu shigar da kara da masu kare wadanda ake zargin, ya dage karar zuwa ranar goma sha uku ga watan gobe don ci gaba da sauraron karar.
Janar Idris Alkali wanda tsohon daraktan gudanarwa ne a shelkwatar rundunar sojin Najeriya, ana kyautata zato an kashe shi ne a yankin Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Pilato.
Ga karin bayani cikin sauti daga Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5