Kotu Ta Dage Shari’ar Likitoci Zuwa Ranar 15 Ga Watan Satumba.

ADAMAWA: Likitoci a FMC Yola sun raba tagwayen da aka haifa a manne da juna

Kotun masana’antu ta Najeriya ta dage sauraron karar dake tsakanin gwamnatin kasar da likitoci zuwa ranar 16 ga watan Satumba 2021.

Kotun masana’antu ta Najeriya ta dage sauraron karar dake tsakanin gwamnatin kasar da likitocin da yanzu haka suke cikin yajin aiki har zuwa ranar 16 ga watan Satumban 2021.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannan shugaban kungiyar likitoci ta kasar (NARD) Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi.

Shugaban kungiyar likitocin yace "a matsayin mu na kungiya mai bin doka , mun je kotu kamar yadda aka gayyace mu amma ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi bata halarci kotun ba, ma’aikatar lafiya ce kawai ta wakilci gwamnatin tarayya.

A cikin sanarwar kungiyar likitocin (NARD) ta roki yan Najeriya da su fahimci dalilin da ya sa yajin aikin ke gudana, yana mai cewa likata mai jin yunwa yana tattare da hatsari.

Yace kungiyar (NARD) na fatan gwamnati za ta yi abin da ya dace don biyan bukatun likitocin domin dakile mummunan halin da bangaren kiwon lafiya zai shiga.

A gefe guda kuma wata sanarwa da ta fito daga daraktan yada labarai na ma’aikatar kwadago da samar da aiki Charles Akpan, ta yabawa manyan likitocin Najeriya da yadda suka nuna dattaku da kuma irin rawar da suke takawa a halin da kungiyar likitoci ta NARD take cikin yajin aiki.