Kotu: Jam'iyyar PDP A Jihar Kano Bata Da 'Dan Takarar Gwamna

A yau litinin babbar kotun tarayya dake Kano ta zartar da hukucin rushe dan takarar gwamnan Kano a karkashin Inuwar Jam'iyyar PDP.

Daya daga cikin wadanda suka nemi Jam'iyyar ta PDP ta tsayar dasu takarar gwamnan Alh. Ibrahim Ali, shine ya gabatar da karar gaban kotun, yana kalubalantar sahihancin hayar da aka bi wajen tsayar Inginiya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar PDP a Kano.

A zamanta na yau, kotun ta ayyana zaben fitar da gwani na dantakarar gwamnan Kano da PDP tayi da cewa, baya kan doka dan haka ta umarci Jam'iyyar ta sake zaben cikin sa'o'i 24 daga lokacin bada wannan umarni.

Dr. Nasiru Adamu Aliyu, lauya ne mai zaman kansa a Kano, kuma ya yi fashin baki dangane da wannan hukunci na kotu a zantawa da wakilin sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari yayi da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu: Jam'iyyar PDP A Jihar Kano Bata Da 'Dan Takarar Gwamna 3'30"