Mataimakin shgugaban majilisar dokokin Jamhuriyar Niger Iro Sani yace lallai an kawo batun gyaran fuska akan hukumar zabe sabo da yanzu hukumar zaben kasar ta din-din-din ce, ba wai sai zabe ya karato ba a girka hukumar zabe kuma mutanen dake cikin ta suna da wa’adi na shekaru 6.
WASHINGTON DC —
Shugaban yana bayani ne a washe garin zaman da majilisar dokoki ta gudanar domin kwaskware dokokin zabe.
To amma da take bayyana matsayin akan wadannan sauye-sauye?
Kotun tsarin mulki kasa tace an sabawa kundin mulkin kasa.
Wannan yasa Salisu Amadu wani dan rajin kare demokaradiyya ya jinjina wa kotun.
‘’Ita kotun ALLAH yayi mata albarka kuma taci gaba da watsar da abubuwan da basu halarta ba, abinda ya shafi kundin zabe da kundin kasa, da dokoki na kasa ba anayin su bane domin sabo da mutum guda, a’a anayin ne sabo da kasa gaba daya domin al’umma ta samu sala’’.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani 2’29
Your browser doesn’t support HTML5